Wata mata ta fashe kuka a filin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti bayan ta zabi APC amma ba’a bata ko sisi ba.
Matar mai suna Muyibat ta bayyana cewa jam’iyyar sun yaudareta kuma mahaifiyar tama ta koka akan wannan lamarin.
A karshe dai an hada matar da wani wakilin APC domin suje su sasanta kansu. Lamarin ya faru ne Sabo karamar hukumar Ijero dake jihar ta Ekiti.