fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Zaben gwamnan Osun: Ku zabi APC don cigabanku da kuma inganta ilimin yaranku bakidaya, cewar Tinubu

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu yaje jihar Osun yau ya taya dan takarar gwamnan jihar Gboyega Oyetola yakin neman zabe.

Inda ya bukaci al’ummar jihar cewa su zabi APC a ranar asabar idan har suna son cigabansu dama na ‘ya ‘yansu bakidaya da kuma iganta ilimi.

Tinubu yayi amfani da wannan damar ya bayyanawa ‘yan jihar cewa shine yafi cancanta ya zama shugaban kasar Najeriya, saboda haka su mara masa baya.

Abokin takararsa Kashim Shettima tare da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El Rufa’i da gwamnan jihar Borno Babagan Zulum da dai sauransu ne suka raka shi jihar Osun din.

Leave a Reply

Your email address will not be published.