fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Zaben jihar Edo: PDP ta fitar da Jadawalin zaben fitar da Gwani

Jam’iyyar Adawa ta PDP ta fitar da jadawalin zabukan fitar da gwaninta a zaben jihar Edo da za’a yi.

 

Sakataren tsare-tsare na jam’iyyar, Col. Austin Akobundu ya bayyana cewa za’a fara sayar da Fom dun neman takarar daga 20 ga watan Mayu inda ranar 2 ga watan Yuni ne ranar karshe ta mayar da Fom din.

 

Ta kuma tsayar da Yuni 4 ga wata a matsayin ranar tantancewar wanda suka cike form din kuma suka mayar dashi sannan a wannan ranane dai duk wani me korafi zai gabatar dashi.

 

Ya kuma kara da cewa zaben dakilai na mazaba guda 3 za’a yishi ne Ranar 9 ga watan Yuni sannan wanda basu yadda ba suna da Ranar 12 ga watan dan daukaka magana.

Karanta wannan  Shugaba Buhari ya nada Aliko Dangote a matsayin shugaban sabuwar kungiyar da zata kawo karshen cutar Malaria a Najeriya

 

Yace ranar 16 ga watan Yuni ne kuma za’a yi zaben kananan hukumomi na wanda zasu zabi wakilan da zasu zabi dan takarar gwamna a zaben. An ware kuma ranar 19 ga wata dan masu korafi.

 

Yace jam’iyyar zata yi zaben dan takarar gwamnanta daga Ranar 23 zuwa 24 ga watan na Yuni. Duk wasu masu koraci suna da damar shigar da korafinsu a Ranar 26 ga watan.

 

Ranar 1ga watan Satumbane PDP zata mikawa hukumar zabe dan takararta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.