fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Zaben shugaban jam’iyyar APC, Shugaba Buhari ya watsawa Tinubu kasa a ido, da wuya ya samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

Bayan goyon bayan da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nunawa Victor Giadom ya zama shugaban jam’iyyar APC,  masu sharhi na ganin cewa wannan ba karamar koma baya bace ga aniyar tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ta samun tikitin takarar shugaban kasa na 2023 karkashin jam’iyyar APC ba.

 

Goyon bayan shugaba Buhari ga Giadom na nufin watsi da Adams Oshiomhole wanda kewa Tinubu biyayya wanda da dadewa Tunibun yayi uwa da marikiya wajan ganin ya zama shugaban APC dan tabbatar aniyarshi ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Da yake sanar da goyon bayan Buhari ga Giadom,  me magana da yawun shugaban kasar,  Malam Garba Shehu ya bayyana cewa shugaba Buhari na bin unarnin doka ne sannan kuma zai halarci taron jam’iyyar da za’a yi yau, Alhamis ta hanyar sadarwar zamani wanda kuma wasu gwamnoni, masu ruwa da tsaki a jam’iyyar zasu halarta.

 

Tun a Ranar Talata, Tinubu yaso ganawa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda ya kira mataimaki na musamman ga shugaban kasar, Tunde Buhari ya samar mai damar ganin shugaban amma ya kiya, kamar yanda Sahara Reporters ta ruwaito.

 

Rahoton yace wasu gaggan jam’iyyar APC ne ke son ganin sun rusa krfin Ikon da Tinubu ke dashi a jam’iyyar da kuma yankin Yarbawa dan hanashi aniyarshi ta samun tikin Shugaban kasa a jam’iyyar a 2023.

Karanta wannan  APC ta gaza domin shugaba Buhari bai damu da ilimin Najeriya ba, cewar daliban Najeriya

 

Wadannan mutane sun hada da Gwamnonin Jigawa, Kaduna, Ekiti, Ondo, Filato, Gombe, Yobe, Kebbi dasu Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, dadai wasu manyan mutane da suka hada da Mamman Daura da Babagana Kingibe, Isa Funtua.

 

Anaso a yiwa Tinubu irin karayar da akawa Bukola Saraki ne, kamar yanda Rahotan ya nunar.

 

Da yake magana akan Tinubu, me magana da yawun shugaban kasa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa ya kamata mutane su gane cewa Tinubu baya cikin kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC dan haka ba zai halarci taron jam’iyyar ba.

Ana kallon Tinubu a matsayin daya daga cikin wanda suka taimakawa shugaba Buhari wajan lashe zabe a shekarar 2015 daga yankin Yarbawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.