fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Zahara Buhari ma tayi murnar cikarsu shekara daya da yin aure: “Nima Nayi dace da miji na kwarai”>>injita

A jiyane mukaji labarin mijin diyar shugaban kasa, Ahmad Indimi yayi murnar cikarsu shekara daya da yin aure, inda ya kara jaddada soyayyarshi ga matar tashi Zahara Buhari kuma ya bayyana cewa yana alfahari da kasancewa mijinta, itama ta fitar da makamancin irin wancan sakon nashi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A cikin sakon nata, Zahara Buhari ta saka wannan hoton na sama da ake gani inda ta bayyana cewa, wannan hoton ya bayyana duk wani abu da nike shirin fada, (Mijina) ka nunamin tsantsar soyayya, ka girmamani kuma kayimin halin kirki/saukin kai, Manzon Allah Annabi Muhammadu (S.A.W) ya fada cewa ” mafi alkhairinku shine wanda yake kyautatawa iyalanshi” nagode Allah nasan kana cikin su(mafiya alherin mutane). Ta kara da cewa itama ta zama cikakken mutum data sameahi a matsayin mijinta kuma itama tana sonshi kuma sun dace da juna.

Karanta wannan  Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele, kuma DSS sun kamashi

Muna musu fatan Alheri.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *