fbpx
Wednesday, March 29
Shadow

Zaharadeen Sani yana kasar Saudiyya dan karo karatu

Daya daga cikin fitattun matasan jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood watau Zaharadeeni Sani, Owner,  ya sanar da cewa yanzu haka yana fadada karatun sa ne a wata makaranta dake garin Riyad can kasar Saudiyya.

Jarumin ya bayyana hakan ne a yayin da yake tattaunawa da majiyar mu ta mujallar Fim game da yadda ba’a ganin sa a fina-finai da yawa a halin yanzu.
jarumin ya kuma bayyana cewa duk da hakan, yanzu haka yana nan akan shirya fim din sa mai suna ‘Sangarta’ a can kasar Saudiyya din.
Daga karshe sai kuma ya godewa masoyan sa da dukkan saunan masu bibiyar harkokin masana’antar ta sa sannan kuma ya sha alwashin cigaba da harkar fim din da zarar ya dawo gida Najeriya.
hausa.naija.ng

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *