Gamuwa da cinkoson motoci kan titi abune me matukar cin rai, musamman idan mutum yana kokarin zuwa wani gurine, na daya dai idan motarka ba me cikakkiyar lafiya bace to zata iya tsayawa anan, idan na’urar sanyaya motarka bata aiki to zakai ta zufa/jiba, ga kuma bata lokaci. wannan labarin cinkoson motocine mafi dadewa da aka taba samu a tarihin Duniya, ya farune a kasar China kuma rahotanni sun bayyana cewa saida aka kwashe kwanaki fiye da goma sannan ya kare.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
A watan Augusta na shekarar 2010 an samu wani mummunan cinkoson motoci akan wani babban titin kasar china da ake kira da National Highway 110, wannan cinkoson nababen hawa da aka samu ya sanya motoci sun jeru akan titi har tsawon kilo mita 100 ko kuma ace mil 60.
Kafafen watsa labarai da yawa irinsu The Daily Telegraph, the Guardian, The Hindu sun bayyana wannan tsaikon motocin da aka samu a kasar China da cewa shine mafi dadewa da tsawo a Duniya.
Da yawan masu motoci sun bayyana cewa a kwana daya sun samu motsa motar sune kawai na tsawon kilo mita daya, wasu kuma direbovin sun bayyana cewa sun kwashe kwanaki biyar a cikin cinkoson motocin kamin daga baya su samu fita.
Mutanen garuruwan dake kusa da titin kasuwa ta bude musu domin kuwa sun rika sayar da kayan biyan bukata a farashi me dan karen tsada, kamar ruwan roba, a cikin gari ana sayar dashi akan kudin China Yan daya amma a ranar an rika sayar musu dashi akan An goma sha biyar, haka taba da indomi da sauran kayan biyan bukata aka rika sayar dasu da tsada.
Dalilin wannan Cinkoson ababen hawa shine wasu manyan motoci da da suke kai kaya cikin kasar Chinan sun bi ta hanyar sannan kuma wasu manyan motocin dake gujewa binciken kayan da suke zaune suma sun biyo wannan hanya, haka kuma akwai gyaran da akeyiwa titin shima ya taimaka wajan kara cinkoson.
Ashe dai ba a Najeriyane kadai ake amfani da wani halin da mutane suka shigaba dan sayar da kaya da tsada, halayyar dan Adam ce, Allah yasa mu dace.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});