fbpx
Monday, December 5
Shadow

Zakarun Turai: Ronaldo ya kafa sabon tarihi bayan cin Dortmund 3-2:Tottenham ta kafa tarihi bayan doke Apoel 3-0

Dan wasan gaba na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya zama dan kwallo na farko da ya ci wa kungiyarsa bal a dukkanin wasanninta na rukuni a gasar zakarun Turai a kaka daya, inda suka doke Borussia Dortmund 3-2.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ronaldo ya daga raga ne a minti na 12, da cin da ya zamar masa na tara a gasar ta zakarun Turai ta bana.
Da hakan yanzu ya ci kwallo 114 a gasar zakarun Turai, kuma ya ba wa abokin hamayyarsa Lionel Messi na Barcelona ratar 17.
Kafin ya ci kwallon Mayoral ne ya fara sa zakarun na Turai a gaba minti takwas da shiga fili, amma kuma minti biyu kafina tafi hutun rabin lokaci sai Aubameyang ya zare daya.
Sannan wasu minti biyun da dawowa fili bayan hutun sai dan wasan na Gabon ya sake daga ragar Real Madrid cikin ruwan sanyi bayan wani dan gumurzu da farko, wasa ya zama 2-2.
Can a minti na 81 ne kuma sai kungiyar ta Spaniya ta tsira da bal ta uku ta hannun Lucas Vazquez.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wasan ya kasance kamar yadda Real Madrid ta yi wa bakin nata shigar sauri ta daga ragarsu har sau biyu cikin minti hudu, haka su ma, suka yi mata, amma cikin kashi dai-dai na wasan.
Kungiyar ta Zidane daman tuni tana ta biyu a rukunin nasu ne a bayan Tottenham, kuma za a iya hada ta a wasan zagaye na gaba, da Roma ko Besiktas ko Paris St-Germain ko Manchester City ko Manchester United ko kuma Liverpool a hadin da za a yi ranar Litinin.
A karon farko Fernando Llorente ya ci wa Tottenham kwallo a wasansa na 17 a kungiyar ta Mauricio Pochettino, wadda ta kammala wasanta na rukuni na takwas (Group H) da nasara 3-0 a kan Apoel, ta kai zagayen kungiyoyi 16 gasar.
Tun kafin wasan na Laraba daman kungiyar ta zama ta daya a rukunin, abin da ya sa ta hutar da wasu daga cikin fitattun ‘yan wasanta ta jarraba wasu.
Llorente, wanda Tottenham ta sayo daga Swansea, ya daga ragar ne a minti na 20 da shiga fili, kafin Son Heung-min ya biyo baya minti 17 tsakani, sai kuma can a minti na 80 Nkoudou ya ci ta uku.
Tottenham, ta zama kungiyar da ta kammala wasan rukuni na gasar ta zakarun Turai ta bana da mafi yawan maki, 16.
Yanzu kuma za ta yi kokarin kawo karshen wasa hudu da ta yi ba tare da nasara ba a gasar Premier idan ta karbi bakuncin Stoke ranar Asabar da karfe 4:00 na yamma agogon Najeriya.
bbchausa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Kalli Bidiyo: Shi Ma Fa Aminu Ya Ci Kudin Talakawa Domin An Dana Shi A Jirgin Gwamnati

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *