fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Zaki ya tsere bayan ya kai wa mai tsaron gandun daji mummunan hari

Wani mutum mai shekara 40 ya tsallake rijiya da baya bayan da zaki ya kai masa hari a lardin Gaza a kudancin Mozambique.

Mutumin ya samu mummunan hari kuma yanzu haka yana jinya a asibiti.

Wani jami’i ya ce zakin da ya kai wa mutumin hari ya kuma tsere daga gandun dajin Limpopo.

Ya ce masu kula da andun daji da hukumomin yankin za su dauki matakan da suka dace kan lamarin da kuma kawar da fargaba ga mutane.

Rikici tsakanin namun daji da mutane ba sabon abu ba ne a mozambique.

Karanta wannan  Gwamnatin tarayya ta jinjinawa gwamna Wike bayan ya cika alkawarin gina babbar makarantar lauyoyi a tarihin Najeriya

A farkon shekarar nan, an kashe wani zaki bayan ya kai wa wasu mutum uku hari kusa da wani gandun daji a lardin Niassa.

Namun dajin da suka fi barazana sun hada da zaki da kada da gwaggon biri da giwaye da kuma kura.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.