fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Zakinnan me yunwa na jihar Kaduna ya Mutu

A kwanakin bayane muka kawo Muku Rahoton wani Zaki me yunwa a jihar Kaduna wanda lamarin ya jawo cece-kuce sosai a shafukan sada zumunta.

 

Sabbin Rahotannin dake fitowa na cewa zakin ya mutu. Wani da yaje Gamji Park inda a nan ne ake ajiye da zakin dan shakatawane ya dauki hotonsa a asirce cikin Watan Nuwamban shekarar 2020 data gabata.

 

Lamarin ya jawo aka hana mutane shiga bangaren da dabbobin suke bayan da masu kare hakkin dabbobi suka yi yunkurin kai musu dauki. Daga baya, Tribune ta ruwaito cewa, an dauke ma dabbobin dake Gamji Park gaba dsya zuwa wani guri da ba’a sani ba.

 

Jaridar ta kai ziyara Gamji Park dan jin yanda lamarin zakin ya kwana. Saidai wani ma’aikacin wajan da baiso a bayyana sunansa ba, ya gaya mata cewa zakin ya mutu, makonni 2 bayan da aka ganoshi cikin yunwa.

Karanta wannan  Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele, kuma DSS sun kamashi

”Yes, I can confirm that the lion has passed on barely two weeks when its footage went viral.

“Some veterinary doctors came to take the lion for treatment later, they came with the shocking news that the lion has died as a result of some complications.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *