Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah tace zaluncin da ake musu ne ya jefa wasu daga cikin su shiga daji su dauki makamai.
Shugaban kungiyar, Alhaji Bello BodejoNe ya bayyana haka a wajan wani taro na musamman da aka shirya.
Ya bayyana cewa amma fa duk da haka, Fulanin sun fi fama da matsalar tsaro fiye da duk wata kabila a kasarnan.
Yace ana zaluntarsu amma ba’a magana sannan kuma du da haka sune ke samarwa Najeriya ci gaba sosai.