fbpx
Monday, June 27
Shadow

Zama da madaukin kanwa: An garkame abokan Abba Kyari guda biyu a gidan yari da ake zargin sunada hannu a cikin zargin da ake masa

Babban kotun birnin tarayya dake jihar Abuja ta yankewa abokan Abba Kyari guda biyu hukuncin shekaru biyu a gidan yari,

Wa’ayanda ake tuhuma sunada hannu dumu dumu a cikin karan da NDLEA ta shigar akan Abba Kyari na zargin shi da safarar kwayoyi.

Mutanen sune na shida dana bakwai da ake zargi a cikin karan da aka shigar na Abba Kyari, kuma an kama sune a tashar jirgin sama na jihar Enugu.

Kuma sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi inda alkali Emeka Nwite ya yanke masu hukuncin shekaru biyu a gidan yari.

Leave a Reply

Your email address will not be published.