Hukumar sojojin Najariya ta bayyana cewa zata dawo da sojojin da suka yi ritaya bakin aiki dan su taimaka a magance matsalar tsaro.
Shugaban sojojin, Lt.-Gen. Faruk Yahaya ne ya bayyana haka ga manema labarai.
Ya bayyana hakane a Rukuba dake Jos babban birnin jihar Filato a wajan wani taro na musamman da aka shirya masa.
Taron an yishine dan wasu sojoji da suka yi ritaya inda kuma shugaban sojojin ya jinjina musu kokarin da suka yiwa kasa yayin da suke aiki.
Janar Maj.-Gen. Ibrahim Ali ne ya wakilci shugaban sojojin a wajan taron.