fbpx
Friday, February 26
Shadow

Zamu Iya Magana ne Kawai Game da Rashin Tsaro, Amma Bamu Da Ikon Magance Shi>>Majalisar Dattawa

Majalisar dattijai, a ranar Talata, ta ce ikonta game da magance matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar na a takaice yake.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana haka a cikin gudummawar da ya bayar ga muhawara a kan wani kudiri mai taken: “Kudirin Makamai Act CAP F28 LFN 2004 (Wanda aka gyara), 2021”, wanda Sanata Uba Sani (Kaduna ta Tsakiya) ya dauki nauyi.
Lawan ya ce masu jajayen kujeru na iya magana ne kawai game da rashin tsaro, muhawara a kai kuma da nacewa cewa an yi wani abu don magance matsalar.
Ya ce ikon aiwatar da manufofi da shirye-shirye da nufin magance kalubalen tsaro ya ta’allaka ne ga bangaren zartarwa.
Lawan ya ce: “A gare mu a Majalisar Tarayya, ya kasance lokaci mai matukar wahala, watakila mafi wahala, saboda mutanenmu na fuskantar wadannan matsalolin na yau da kullum na tsaro.
“Tambayar koyaushe ita ce ‘me kuke yi ne?’
“Kuma abin takaici, majalisar dokoki ta takaita cikin abin da za ta iya yi.
“Ba za ta iya aiwatarwa ba amma tana iya magana, tattaunawa, muhawara da kuma nacewa akan maganar.
“Na yi imanin cewa wannan bangaren zartarwa a shirye suke don yin wani abu don inganta yanayin tsaro kuma yanzu muna ganin wata hanya ta daban kuma ingantacciya watakila ƙarshen rashin tsaro a ƙasar nan ya zo.
“Kwanan nan, mun ga Mai ba da Shawara kan Harkokin Tsaro yana aiki tare da Shugabannin Tsaro da sauransu a cikin tsari yadda ya kamata.
“Muna addu’ar wannan ya dore kuma a gare mu zamu basu dukkan goyon baya.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *