fbpx
Saturday, September 23
Shadow

Zamu kai kungiyar kwadago ta NLC kotu saboda karyar data mana cewa an baiwa kowannen mu tallafin Naira Miliyan 100>>Inji ‘Yan Majalisar tarayya

Majalisar tarayya ta yi barazanar kai kungiyar kwadago ta NLC kotu saboda zargin da NLC din ta yi cewa an baiwa kowane dan majalisa tallafin Naira Miliyan 100.

 

A baya dai an ji kakakin NLC, Christopher Onyeka ya bayyana cewa an baiwa ‘yan majalisar Naira Miliyan 100 kowanensù dan rage radadin cire tallafin man fetur.

 

Saidai kakakin majalisar, Yemi Adaramodu ya karyata wannan ikirari, inda yace sam hankali ba zai dauka ba.

 

Majalisar tace karyace kawai da ‘yan Media da kima kokarin saka majalisar cikin damalmalar tsana tsakaninta da talakawa.

 

Dan haka majalisar tace a yi watsi da wannan ikirari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *