fbpx
Monday, August 8
Shadow

Zamu kare kanmu daga fulani makiyayan Idan Shugaba Buhari da Abiodun sun gaza – Sarkin Ogun

Olu na Ilaro Kehinde Olugbenle, ya gargadi Gwamnatin Najeriya da kuma ta Jihar Ogun kan illar da ke tattare da kisan mutane a Yewaland da Fulani makiyaya ke yi.

Wasu da ake zargin makiyaya ne, a daren Juma’a, sun mamaye Igbooro, Oja-Odan da ke cikin Karamar Hukumar Yewa ta Arewa a jihar, sun kashe mutane uku sannan raunata biyu.

Makiyayan sun mamaye kauyen kusa da Eggua a Oja-Odan da misalin karfe 11 na dare, inda suka yi ta harbi ba kakkautawa tare da kona gidaje uku da rumbunan ajiya a kauyen.

Karanta wannan  Hallau rundunar sojin sama ta sake kashe shugaban 'yan ta'addan jihar Katsina tare da tawagarsa

A martaninsa, Sarkin yace masarautar ta yi tir da kashe-kashen a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar mai taken, “Dakatar Da Lokacin tTashin Bam Kafin Lokacin Ya Kure” wanda ya aike wa Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Dapo Abiodun.

A karshe Sarkin ya yi gargadin cewa idan har Shugaba Buhari da Gwamna Abiodun sun gaza baiwa mutanen yankin kariya to mutanen zasu fara kare kansu daga hare-haren fulani makiyaya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.