Gwamnatin tarayya ta bayar da tabbacin kubutar da wanda ‘yan Bindiga suka sace daga jirgin kasan dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja.
Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ne ya bayar da wannan tabbaci inda yace ba zasu yi kasa a gwiwa ba har sai sun ga an kubutar da mutanen.
Ya bayyana hakane ranar Alhamis a wajan ganawa da manema labarai a babban birnin tarayya, Abuja.
Ya bayyana cewa, ma’aikatarsa na ganawa da jami’an tsaro kan ceto mutanen, Saidai yace ba za’a fadi irin shirin da ake ba dan kada hakan ya kawo matsala.
Wasu ‘yan uwan wadanda aka sace din dai sun je wajan taron inda suka fara Zanga-Zanga.