Yan bindigar da suka tayar da bam a jirgin kasa a jihar Kaduna sun bayyana cewa zasu kashe mutanen dake hannunsu idan har gwamnati bata biya masu bukatunsu ba.
Sun bayyana hakan ne a wani bideyo da suka saki inda suka ce zasu mayar da hanyar kamar abbatuwa, don su kashe mutane ba komai bane a wurin su.
Kuma sunce gwamnati ta san abinda suke bukata, domin ba zasuyi garkuwa da mutanen ba don a basu kudin fansa ba, suba kudi suke bukata ba.