Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, masu kashe-kashe a jihohin Inyamurai su jiraci martani me zafi.
Shugaban ya bayyana hakane a sanarwar da ya fitar ta bakin kakakinsa, Malam Garba Shehu inda yace yana Allah wadai da kashe wata mata da ‘ya’yanta 4 musulmai kuma ‘yan Arewa da ‘yan Bindigar suka yi.
Shugaban ya sha Alwashin kawo karshen matsalar tsaron a yankin dama kasa baki daya.