fbpx
Monday, August 15
Shadow

Zamu siyowa sojoji motocin yakin da ba’a taba siyo irinsu ba dan yakar ayyukan ta’addanci>>Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa suna shirin siyowa sojojin Najeriya motocin yakin da ba’a taba siyo irinsu ba a tarihin Najeriya dan gamawa da ‘yan Bindiga.

 

Gwamnatin ta dauki wannan matakine bayan ganawa tsakaninta da geamnonin Najeriya.

 

Gwamnatin ta kuma ce za’a gaggauta kera motocin da sauran kayan aikin da zata siyo kamar yanda kamfanin da zai yi aikin ya sanar da ita.

 

Matsalar tsaro dai sai kara ta’azzara take a Najeriya duk da kokarin da mahukunta ke cewa suna yi dan maganceta

Leave a Reply

Your email address will not be published.