fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Zamu taimakawa ci gaban Dimokradiyya a Africa>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Najeriya zata taimakawa ci gaban Dimokradiyya a Nahiyar Africa.

 

Shugaban ya bayyana hakane a yayin da yake karbar bakuncin shugaban kasar Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore a fadarsa dake Abuja.

 

Shugaban ya bayyana cewa, duk kasar dake shirin zabe, Najeriya zata taimaka mata wajan ganin an yi nasa a zaben yace suna saka ido sosai kan kasashen Africa da harkar zabukansu.

A nasa bangaren shugaban kasar Burkina Faso ya bayyana cewa ya zo Najeriya ne a ziyarar kwana daya dan su tattauna matsalolin kasuwanci dake tsakanin kasashen. Ya kuma jinjinawa shugaba Buhari akan yaki da ta’addanci da kuma yanda yake yaki da cutar Coronavirus/COVID-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published.