fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Zamu zauna da shugaba Buhari,Obasanjo, Atiku da Tinubu dan tattauna yanda za’a bamu mulki a 2023>>Kungiyar kare muradun Inyamurai

Kungiyar matasa masu kare muradun Inyamurai me sunan OYC ta bayyana cewa tuni ta fara shirye-shiryen ganin cewa dan kabilar ya dare kan mulkin shugabancin kasarnan a shekarar 2023.

 

Tace tana jirane a gama da matsalar Coronavirus/COVID-19 dan ta fara aiki haikan wajan ganin burinta ya cika.

 

Kungiyar tace zata zauna da shugaban kasa,Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da Tsohon shugaban kasa,Olusegun Obasanjo da kuma jiho a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu dan su tattauna batun.

 

Sun kara da cewa hana wani bangare mulki a kasarnan yana da matsala dan kuwa idan aka ce ba za’a basu mulki ba to maganar neman kafa kasarsu ta Biafra zata ci gaba, hakanan suma Yarbawa tabbas zasu ci gaba da neman kafa kasar Oduduwa.

Karanta wannan  Zan iya rantsuwa da alkur'ani cewa Atiku ne ya lashe zaben shekarar 2019, cewar Buba Galadimar

 

Daily post ta ruwaito sanarwar na cewa ya kamata Najeriya ta mutunta alkawarin da aka yi na cewa kowane yankin kasarnan ya rika taba mulki duk da cewa dai alkawarin ba’a rubuce yake ba.

 

Sun kuma ce Allah ya san dailin da yasa ya bar tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon a raye dan ya kawo hadun kai a kasarnan domin shine zasu sama ya zabar musu dan kabilar su mutumin kirki wanda zai zama dan takarar shugaban kasa, shskaru 50 bayan yakin basasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.