Mawakin Najeriya Charles Oputa, wanda akafi sani da Charly Boy ya bayyana cewa zai bar Najeriya idan har Atiku Abubakar ko Bola Tinubu yaci zabe a shekarar 2023.
Charly Boy ya bayyana hakan ne a kafar sada zumuta ta Twitter bayan APC ta tabbbatar da cewa Bola Ahmad Tinubu ne ya lashen zabenta na fidda gwani.
Inda Charly Boy yace zai bar Najeriya kawai yaje Ghana ya roqisu katin zama dan kasa idan har Atiku ko Tinubu yaci zabe, domin Buhari ya zama tamkar bawa.