Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, zai cire duk ministan da ya gaza aiki yanda ya kamata.
Tinubu ya kara baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa ba zai basu kunya ba.
Tinubu yace yanawa tattalin arzikin Najeriya garambawul na dindindin ne.
Yace kuma zai gudanar da gwamnatinsa inda zai baiwa kowa damar aiki musamman wadanda suka hidimta masa.