fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Zan dauki karin sojoji da ‘yansanda idan na zama shugaban kasa>>Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, zai dauki karin sojoji da ‘yansanda idan ya zama shugaban kasa a 2023.

 

Yace zai yi hakane dan ganin ya yaki ‘yan Bindiga.

 

Atiku dake neman takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP ya bayyana hakane a Akure ranar Lahadi da dare yayin ganawa da wakilan jam’iyyar da zasu fitar da dan takarar ta.

 

Atiku ya kuma ce zai samar da makamai na zamani ga sojoji da ‘yansandan idan ya kai ga mukamain shugaban kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.