Jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya kaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa da yammacin jiya.
Bola Tinubu ya kuma jinjinawa shugaba Buharin kan yanda bai yi katsalandan ba a harkar zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka yi.
Sannan yayi alkawarin zai dora daga inda Buhari ya tsaya idan yayi nasara a zaben shekarar 2023 ya zama shugaban kasa.