fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Zan Gina Sabuwar Nijeriya Tare Da Hada Kan ‘Yan Kasa, Cewar Gwamna Bala Muhammad

Gwamnan jihar Bauchi kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya yi alkawarin hada kan Nijeriya tare da sake fasalin shugabanci na gari idan har aka ba shi dama na shugabanci.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yau a lokacin da yake zantawa da masu ruwa da tsaki da wakilai na jam’iyyar PDP a jihohin Neja da Taraba inda ya kara da cewa ya shirya tsaf Domin kawo sauyi ga Yan Nijeriya.

A cewar Gwamnan Muna ankare da halin da Najeriya ke ciki a karkashin jam’iyyar APC, Wanda ta lalata komai.

Ya ce gwamnatinsa za ta kasance mai son hadin kan kasa, da yaki da kabilanci ko Bambanci addini , ya kara da cewa a matsayinsa na mai bin dimokradiyya, zai tabbatar da daidaito.

Gwamnan Yace akwai bukatar kawo a gyara ta fuskan zaman takewa wanda zai kawo cigaba ga hadin kai da bunkasar tattalin arziki,

Domin ganin an dawo da martabar Nijeriya tare da samar wa ‘yan kasa shugabancin Nagari.

Da yake jawabi Gwamnan jihar Taraba Diarus Dickson Ishaku ya ce Gwamna Bala Mohammed haziki ne mai bajinta da ya yi kokari matika lokacin da ya rike mukamin babban Ministan birnin tarayya Abuja, Yace Dukkanin abinda yake fada na son gina kasa da hada kan Yan kasa ya aiwatar da shi a birnin tarayya Abuja lokaci Yana Minista.

Karanta wannan  Taron dangi aka min>>Sanata Dino Melaye kan faduwa zabe

Kuma yanzu haka yana kan shimfida Ayyukan alheri a jihar Bauchi. Domin haka wajibi ne mu mara masa baya a matsayin sa na Dan Yankin mu. Zamu bayar da Dukkanin gudunmawar da ta dace.

A nasu jawabin, cikin masu ruwa da tsaki da wakilan jam’iyyar PDP na jihohin sun bayyana amincewar su da takaran Gwamna Bala tare da yin alkawarin Bashi goyon bayan da ya kamata Don hada kai a ceto Nijeriya.

Daga Lawal Muazu Bauchi
Mai Taimakawa Gwamnan jihar Bauchi kan Sabbin Kafafen Yada Labarai na zamani

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.