fbpx
Sunday, December 4
Shadow

Zan hada tawaga ta musamman domin magance matsalolin Nageriya, idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa – Gwamna Tambuwal

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Gwamna Aminu Tambuwal, ya yi alkawarin hada tawagar kwararrun masana tattalin arziki don magance matsalolin tattalin arzikin kasar, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Tambuwal a ganawar daban-daban na tuntubar juna da jam’iyyar PDP a majalisar dattawa da ta wakilai da kuma kwamitin amintattu na PDP a Abuja, ya kuma ce zai mayar da Najeriya daya daga cikin kasashen da suka ci gaba ta fanne daban-daban.

A bangaren tsaro kuwa, Tambuwal ya ce idan aka zabe shi zai magance matsalolin rashin tsaro da suka hada da yunwa, fatara da kuma karancin ilimi.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *