fbpx
Thursday, August 11
Shadow

ZAN IYA HUDA HANCI SABODA KWALLIYA GA MIJINA ?

ZAN IYA HUDA HANCI SABODA KWALLIYA GA MIJINA ?

An tambayi sheikh Ibnu Uthaimin akan wannan mas’alar ta huda Hancı sai yake cewa: Huda Hancı zai iya zama canza halittar Allah, amma idan Garin da matar da ta huda hancin take ana yın ado a hanci, ta yadda hakan ya zama al’ada, to babu laifi ayi hakan. Duba: Majmu’u Fatawaa Ibnu Uthaimin 11/137.

Haka nan an tambayi Sheik Abdul Muhsin Al’abbad akan haka a darasinsa da yake gabatarwa a Haram, sai ya ce babu laifi akan haka.

Bisa Abin da ya gabata ya halatta matar BAHAUSHE ta huda hancinta saboda ta sanya abin kwalliya tun da al’adarsu ce, saboda ya tabbata sahaban Annabi s.a.w. mata suna huda kunnansu suna sanya ‘yan kunnaye Kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba: 98 yake nuni zuwa hakan.

Allah ne mafi sani.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.