Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya lashi takobin magance siyasar jagaliyanci da ta addabi jihar tsawon lokaci, inda ya bayyana hakan cikin manyan abunda zai saka a gaba a aikin da zaiyi a jihar.
A makwan da ya ga bata ne Jihar Kano ta samu sabon kwamishinan ‘yan sanda bayan Samun karin matasyin da tsohon kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Habu Sani ya samu wanda ya zama mataimakin Safeto Janar na ‘yan sanda na Kasa.