Friday, June 26
Shadow

Zan kori duk ministan da baya aiki yanda ya kamata>>Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, zai kori duk ministan da baya aiki yanda ya kamata.

Tinubu ya bayyana hakane a ganawar da yayi da kungiyar dattawan Arewa ta ACF da yammacin ranar Alhamis.

Yace zai ci gaba da yin aiki iya kokarinsa dan ci gaban Najeriya.

Ya bayyana cewa, yana godewa ‘yan majalisar zartaswarsa kan kokarin da suke amma zai rika dubawa yana tankade da rairaya dan gano wanda basa aiki yanda ya kamata dan canjasu.

Karanta Wannan  Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *