fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Zan mayar da NTA kamar CNN idan aka ba ni rancen ‎₦181b>>Lai Mohammed

Ministan watsa labaran Najeriya, Lai Mohammed, ya sha alwashin mayar da gidan talbijin din kasar, NTA, tamkar gidan talbijin na CNN da ke Amurka idan majalisar dokokin kasar ta bari ya karbo rancen $500m, kwatankwacin kusan naira biliyan 181.

Kafofin watsa labaran Najeriya, ciki har da jaridar Guardian, sun rawaito cewa ministan ya bayyana haka ne lokacin da ya je gaban kwamitin da ke kula da karbo bashi a ciki da wajen kasar na majalisar dattawa.
Ya kara da cewa yana so su amince a karbo bashin ne daga cikin $29.96b da Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar ta amince ya karbo domin gudanar da manyan ayyuka a kasar.
‘Yan Najeriya da dama sun yi ta yi wa ministan shagube a shafukan sada zumunta, inda yanzu haka yake cikin manyan abubuwan da aka fi tattaunawa a kansu a shafin Twitter.
Wani mai amfani da Twitter, Olusegun Iselaiye, ya ce ko da NTA za ta samu ninkin kudin da Lai Mohammed yake so a ranto, ba za ta zama tamkar gidan talbijin mai zaman kansa na kasar Channels TV ba, ballantana CNN.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Darajar Naija ta kara faduwa kasa inda ake sayar da Dala daya akan Naira N 600


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.