fbpx
Friday, August 12
Shadow

Zan mayar da Zamfara jihar datafi kowace zaman lafiya a Najeriya, cewarGwamna Matawalle

Matawallen Zamfara ya bayyana cewa kafin ya sauka a mulki sai ya samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Zamfara ta kasance daga daga cikin manyan jihohin da ‘yan bindiga suka takurawa a fadin Najeriya, inda har suka kore wasu al’ummar a kauyukansu.

Gwamnan jihar, Bello Matawalle ya bayyanawa manema labarai a ranar talata cewa zai mayar da jihar tafi kowace zaman lafiya a Najeriya.

Inda kuma ya bukaci gwamnatin tarayya ta karawa jami’ai shekarun ritaya zuwa 70 domin zai taimaka masa wurin cika burin nasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.