fbpx
Saturday, June 25
Shadow

Zan Rungumi Kaddara Na Koma Gida Idan Aka Kayar Da Ni A Zaben Fidda Gwani, Cewar Tinubu

Daga Comr Abba Sani Pantami

Jagoran jam’iyyar APC na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya ƙara sabuwar magana kan abin da zai yi idan ya rasa tikitin APC.

A wani Bidiyo da Jubril Gawat, mai taimaka wa gwamnan Legas ta bangaren Midiya, ya saki a shafinsa na Twitter, Tinubu a cikin yaren Yarbanci ya ce ya shirya wa zaɓen.

“Na kammala duk wani shiri na lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a APC, kowa ya kwantar da hankalinsa, a cewar Bola Ahmed Tinubu.

Karanta wannan  Wani Mejo Din Sojan Nijeriya Ya Yi Wa Kansa Kisan Gilla A Kaduna

Sai dai tsohon gwamnan Legas ɗin ya kuma bayyana cewa idan Allah ya sa bai samu nasara ba zai rungumi kaddara ya koma gida.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.