Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa, idan aka zabeshi shugaban kasa a shekarar 2023 zai samar da kwararrun mutane da zasu warware matsalolin Najeriya.
Tambuwal ya bayyanawa wasu ‘yan jam’iyyarsu ta PDP ne haka a Abuja inda yace kuma zai gyara Najeriya.
Gwamna Tambuwal ya kuma ce zai magance matsalar tsaro, yunwa da talauci.