Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya bayyana cewa zai samar da tsaro a Najeriya kamar yadda yayi a Kogi idan yayi nasarar zama shugaban kasar.
Kuma yace zai yi kokarin samar da ayyuka domin matasa su samu abinyi kuma a rage yawan talaucin da ‘yan kasar ke fama dashi.
Gwamnan ya kara da cewa baya shakkar Tinubu da Osinbajo, kuma dalili shine shima ya yadda da kanshi cewa zai iya yin nasarar lashe zaben.