fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Zan sayi bindigar amma abin kunya ne gwamnatin Zamfara tace mu kare kanmu saboda hakkin sune, cewar wani manomi dan jihar Zamfara

Al’ummar jihar Zamfara sun fara tofa albarkacin bakinsu kan maganar da gwamnatin jihar tayi na cewa su sayi bindugu don kare kawunansu.

Inda wani manomi dake Talata Marafa, Aminu Haruna ya bayyana cewa wannan maganar da gwamnatin tayi ta nuna cewa ‘yan bindigar sunfi karfinta yanzu.

Kuma hakan abin kunya ne domin hakkin su ne su kare rayukan al’ummarsu, amma shi yace zai sayi bindigar da zarar sun fara bada damar domin ya kare kansa da iyalansa.

Inda ya kara da cewa a matsayin shi na manomi dole ya rika zuwa gona a wannan yanayin saboda haka zai sayi bindigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.