fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Zan tabbatar an bi wa Hanifah haƙƙin ta>>Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya tabbatar wa da iyayen Hanifah cewa zai taimaka musu wajen ganin cewa an bi musu haƙƙin ƴar su.

Kwankwaso ya bada tabbacin ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga mahaifan Hanifah Abubakar, ƴar shekara 5 da malamin ta ya yi mata kisan gilla a Kano a jiya Lahadi.

Kwankwaso ya yi addu’ar neman rahma ga Hanifah, in da ya roƙi Allah da ya baiwa mahaifan nata hakuri da juriya a kan ibtila’in da su ka tsinci kansu a ciki.

Tsohon Gwamnan ya tabbatar musu da cewa duniya baki daya na tausaya musu a bisa kisan gillar da a ka yiwa ƴar su ƙwaya ɗaya tilo, inda ya shaida musu da cewa za a bi diddigin lamarin har sai an tabbatar da bi musu haƙƙin ƴar ta su.

Karanta wannan  Da Duminsa:'Yan Bindiga sun sace babban dan Siyasa a Arewa sun kashe me tsaronsa

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Kwankwaso ya samu rakiyar ɗan takarar gwamnan Kano na PDP a zaben gwamna na 2019, Abba Kabiru Yusuf da sauran muƙarraban sa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.