Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya baiwa ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen waje tabbacin cewa gwamnatinsa zata basu kariya da kare muradunsu.
Shugaban ya bayyana hakane a kasar Sufaniya yayin ganawa da ‘yan Najeriya dake zaune a kasar.
Shugaba Buhari yace kuma yana kiran ‘yan kasuwar kasar ta Sufaniya su shigo Najeriya dan zuba jari.