fbpx
Thursday, February 9
Shadow

Zan taimaka a kayar da PDP a zaben 2023, cewar gwamna Wike

Gwamnan jihar Patakwal, Nyesom Wike da shugaban jam’iyyarsu ta PDP basu da niyyar sasanci a tsakaninsu yayin da suke cigaba da sukar junansu a bainin jama’a.

Wike ya bukaci shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu yayi murabus kamar yadda ya fada a baya cewa zai yi murabus idan ba dan kudu ne ya samu tikitin jam’iyyar na shugaban kasa ba.

Amma Ayu yace yara ne suke cewa yayi murabus wa’yanda basu san asalin yadda aka kirkiri jam’iyyar PDP ba.

Gwamna Wike ya mayar masa da martani cewa yaran nan dai sune suka dakko shi daga rana har ya zama shugabansu, kuma tunda so yake PDP ta fadi zabe zasu bada gudun mawa.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *