Daga Abubakar A Adam Babankyauta
Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana”Aniyar shi ta neman zama magajin shugaba Buhari 2023
Sanata kwankwaso ya bayyana”Aniyar shi ta tsayawa takarar neman Mulkin Nijeriya 2023 tare da irin ayyukan da zai gudanar idan ya zama shugaban kasa.
Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabiu Musa kwakwaso ya bayyana cewa zai mayar da hankali wajen farfado da fannin ilimi, inganta tsarin kiwon lafiya, bunkasa tattalin arziki ta hanyar gyara bangaren sufurin jiragen sama, samar da guraben aikin yi ba tare da karbo rance daga kasashen waje ba idan har aka zabe shi a matsayin shugaban Nijeriya.
A cewar Kwankwaso APC mai mulkin Nijeriya da kuma jam’iyyar adawa ta PDP sun gaza kuma kamata ya yi ‘yan Nijeriya su duba sauya jam’iyya ta NNPP don kai su ga gaci.
A cewar Kwankwaso ba wa yaran marasa karfi ingantaccen ilimi zai rage matsalolin da ake fuskanta a Nijeriya kuma wannan shine zai zamo daya daga cikin abubuwan da gwamnatin shi zata sa’a gaba.
Baya ga bangaren ilimi, sufurin jiragen sama da kiwon lafiya, Kwankwaso ya ce idan aka zabe shi, gwamnatinsa zata mayar da hankali kan arzikin da Nijeriya ke da shi wajen gina ta a maimakon zuwa kasashen waje ciyo bashi da jikokinsa zasu rika biya nan gaba sakamakon rashin kishin wasu shuwagabanni baya.
Acikin jawabin da kwankwaso ya saki”Majiyar mu ta sanar mana da cewa kwankwaso yace APC batayi Adalci ba idan har taki mika takarar ta yankin kudu domin akwai yarjejeniyar hakan a shekarun baya.