fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Zan wanke taɓargazar Nasir El-Rufai idan na zama gwamnan Kaduna a 2023>>Shehu Sani

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a zaɓen 2023.

Yayin hira da wani gidan rediyo a jihar, sanatan ya yi alkawarin wanke abun da ya kira ”tabargazar gwamnan jihar mai ci Nasir El-Rufa’i” idan ya yi nasara.

”Duk wanda ya musguna wa jama’a ya ƙuntata musu bai cancanci ya samu kowacce irin dama ba, domin duka addinanmu sun girmama ɗan adam”.

Shehu Sani ya ƙara da cewa a yanzu ya rage wa jam’iyyar PDP ta haɗe kan ƴaƴanta don ƙwatar mulki a hannun APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published.