Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, zai yi abinda yafi na Buhari wajan inganta Najariya idan aka zabeshi a matsayin shugaban kasa.
Tinubu yace zai mayar da hankali wajan samarwa da matasa ilimi da kuma samar da tsaro.
Tinubu ya bayyana hakane a wajan yakin neman zabensa a Kano ranar Laraba. Ya kuma yabawa gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike kan kalubalantar takarar shugaban kasa ta Atiku Abubakar.
Yace bai kamata a yadda da PDP ta kara karbar ragamar kasarnan ba.