fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Zan Yi Azumi Guda Bakwai Domin Rokon Allah Ya Kawo Mana Karshen Mulkin Jam’iyyar APC A Nijeriya>>Matashin Dan Kasuwa Musa Suleiman Sarki

Wani matashin dan kasuwa a jihar Gombe, mai suna Musa Suleiman Sarki, ya dauki alwashin yin azumi guda 7 tare da rokon Allah ya kawo wa al’ummar Nijeriya karshen mulkin jam’iyyar APC.

 

Dan kasuwa Musa Sarki, ya sha alwashin fara azumin ne daga gobe Juma’a, kan yadda gwamnatin Nijeriya ke gallazawa talakawan kasar wajan tsadar kayan abinci, man fetur, wutar lantarki, tare da kasa cika musu alkawuran da gwamnatin kasar ta dauka a lokutan yakin neman zabe.

 

Idan baku manta ba, kwanan nan gwamnatin Nijeriya ta kara kudin man fetur da wutar lantarki duk da halin da al’ummar kasar ke ciki na tsadar kayan abincin da al’umma ke fama dashi, wanda hakan yasa al’umma da yawa suke cigaba da fadin munanan kalamai tare da kokawa ga gwamnatin kasar.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

 

Masu neman karin bayani game da alwashin azumin da matashin ya dauka, za su iya tuntubar shi ta wannan lambar; 08108566460.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.