Gwamnan jihar Filato kuma shugaban kungiyar yakin neman zabe ta dan takarar shugaban kasa na APC, Simon La Long yasha alwashin taimakawa Tinubu ya lashe zaben shekarar 2023.
Simon La Long ya bayyana hakan ne a ranar alhamis yayin dayake ganawa da manema labarai a tashar jirgin sama ta Yakubu Gowon a jihar Jos.
A jiya ranar alhamis shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya bayyana cewa sun gabatarwa shugaba Buhar La Long a matsayin shugaban kungiyar kamfe ta Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima.
Kuma La Long ya nemi ‘yan Najeriya cewa kar su bari rikicin addini yasa su zabi shugaban da bai dace ba, yace Najeriya daya ce kuma matsala daya suke fuskanta saboda haka su ajiye batun addini a gefe su zabi shuwagabanni na gari.