fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Zan zagaye jihar Katsina da katanga idan na zama gwamna>>Inji dan takara

Zan katange Jihar Katsina idan na zama gwamna, in ji ɗan takara

Tsohon ɗan takarar gwamna a Jihar Katsina a jam’iyar APGA a zaɓen 2015, Abdullahi Umar Tsauri ya ci alwashin katange ɗaukacin jihar idan ya zama gwamna.

Tsauri, wanda yanzu ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina ne a Jam’iyar APC, ya baiyana haka ne a yayin taron masu ruwa da tsaki da kuma ƙaddamar da kwamitin yaƙin zaɓen sa.

Ɗan siyasar ya ci alwashin kawo ƙarshen kashe-kashe da garkuwa da a ke yi da mutane tsawon shekaru a jihar, inda ya ce ɗaya da ga cikin dabarun samar da zaman lafiya, shine zai katange gaba ɗaya jihar.

Karanta wannan  Mai kudin Duniya, Elon Musk ya sayar da hannun jarinsa na dala biliyan 6.9 na kamfanin Telsa, shin ko meye dalili?

“Zan ƙirkiro da wata dabara ta katange gaba ɗaya bodar Katsina da Zamfara da Kaduna kuma zan ɗauki ƴan vigilante 500 a kowanne bangare sa ke fama da rashin tsaron,” in ji Tsauri.

Daga Daily Nigerian.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.