fbpx
Monday, August 15
Shadow

Zanga Zangar ENDSARS ce ta taimakawa ‘yan ta’adda suka kai hari gidan kurkuku na Kuje, cewar ministan cikin gida

Ministan cikin gida, Rauf Arẹgbẹsọla, ya  bayyana cewa zanga-zangar ENDSARS ce ta taimakawa ‘yan ta’addan ISWAP suka kai hari gigan kurkuku na Kuje.

A makon daya gabata ne ‘yan ta’addan na suka kai harin a gidan kurkukun dake babban birnin tarayya, Abuja.

Inda suka sako mutane da dama da aka kama aka kulle a ciki hadda ‘yan Boko Haram guda 64.

Kuma ministan cikin gida yace duk ENDSARS ce ta kawo hakan dama wasu haren haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa alummar Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.