ZARGIN GANIN DAN HISBA DA MATAR AURE A OTAL: A Karshe Dai Ma’aikacin Radio Freedom Yusuf Ali Abdallah Ya Nemi Afuwar Jami’in Hisba Sani Rimo.
Daga Imam Indabawa Aliyu
A shekarar da ta wuce ne aka yi ta cece-kuce cewa an ga wani babban jami’in hukumar hisba ta jihar Kano wato Sani Rimo tare da matar aure a Otal, wanda hukumar ‘yan sanda ta bakin kakakinta Abdullahi Haruna Kiyawa ta wanke jami’in cewa ba gaskiya ba ne zargin ganinsa da matar aure a Otal.
Cikin wadanda suka yada wannan zargi akwai gidan rediyo na “Freedom” ta bakin ma’aikacinta Yusuf Ali Abdallah. Sai dai bayan ma’aikacin ya kasa tabbatar da maganganunsa a Kotu a karshe ya nemi afuwar Sani Rimo Jami’in hukumar hisba.