fbpx
Saturday, December 3
Shadow

Zawarawan Ronaldo na juya masa baya, Barcelona ba za ta yi cefane ba

A watan Janairu Manchester United za ta sake zawarcin Memphis Depay domin dawo da dan gaban na Barcelona na kasar Netherlands Old Trafford, inda ya bari a 2017.

Newcastle United ba ta da niyyar zawarcin Cristiano Ronaldo, bayan ya raba gari da Manchester United.

Ita ma Chelsea kusan ba ta da niyyar neman Ronaldon a yanzu duk da cewa babu wani kwantiragi a kansa duk da a baya ta nuna sha’awa a kansa.

Manchester United din kuma tana tattaunawa kan ko ta maye gurbin Ronaldon dindindin a watan Janairu ko kuma ta bari har zuwa bazara ta dauko wani dan wasa na wucin-gadi a yanzu kamar yadda ta yi lokacin da ta dauki Odion Ighalo dan Najeriya a 2020.

Manchester United ta yi amanna yawan magoya bayan da take da su a duniya zai sa  masu son sayen Liverpool su karkata wajen sayen kungiyar ta Old Trafford.

Shi kuwa attajirin nan na Birtaniya Sir Jim Ratcliffe zai taya Manchester United, bayan da a baya da ya biloniyan ya nuna sha’awarsa ta cinikin a watan Oktoba sai iyalan Glazer masu kungiyar suka ce ba su da niyyar sayar da ita.

Haka kuma tsohon dan wasan Manchester United din David Beckham a shirye yake ya tattauna da masu son sayen kungiyar.

Manchester United din kuma tana son dan wasan Bayer Leverkusen Moussa Diaby, na Faransa ya maye gurbin Anthony Martial a kungiyar.

Leeds United na tuntubar AC Milan inda ta nemi a rika sanar da ita a kan matsayin dan wasan Belgium Charles de Ketelaere, mai shekara 21.

West Ham na ganin za ta rasa dan wasanta na tsakiya Declan Rice, ga wata kungiyar da za ta fafata a gasar zakarun Turai a shekara mai zuwa duk matsayin da Hammers din suka kai a kakar nan.

Dan gaban Sifaniya Marco Asensio, ya ce yana son ci gaba da zama a Real Madrid, duk da cewa kwantiraginsa zai kare a karshen kaka.

Barcelona ta gaya wa kociyanta Xavi za ta iya sayen sabbin ‘yan wasa ne kawai a watan Janairu idan wasu ‘yan wasan suka tafi.

Atletico Madrid na son sayen dan wasan Borussia Monchengladbach da Faransa Marcus Thuram.

Sabbin masu son sayen Everton ‘yan Amurka na dab da shirin kama iko da kungiyar gaba daya sakamakon abin da ke wakana a bayan fage.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *