fbpx
Sunday, December 4
Shadow

Ziyarar shugaba Buhari a Kano: Da ayyukan daya gudanar a yau

A yaune shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Kano, inda akewa kallon tushen siyasarshi saboda irin tarin masoya da yake dasu a jihar, bayan ya sauka a filin jirgi, shugaba Muhammadu Buhari, ya wuce fadar me martaba sarkin Kano, Muhammad Sunusi na II inda ya kai mai gaisuwar bangirma.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Bayannan, shugaba Buharin ya shaida yafewa fursunonin gidan yarin kurmawa dake jihar kanon su dari biyar da gwamnatin jihar, karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi, wasu daga cikinsu an yafe musu laifukan da sukayi, wasu kuwa gwamnatin jihar ta biya kudin tarar da aka yanke musu.
Shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa fursunonin kudin motar da zaikaisu gida, haka kuma yace ya tambayi daya daga cikin fursunonin shekarunshi nawa kuma ya shaidamai cewa shekarunshi sha tara, shugaba Buhari yace gwamnatinshi zata bayar da muhimmanci sosai wajan ganin ana kulawa da horar da mazauna gidan yari da kuma kokarin canja musu dabi’a, domin, kamar yanda yace, idan akwai masu shekaru sha tara a gidajen yarinmu sannan kuma aka barsu babu kulawa to rayuwarsu ta lalace kenan.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Aisha Buhari ta janye kararda ta kai Aminu Muhammad

 Daganan kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wuce Asibitin Giginyu, wanda aka sawa sunanshi, inda ya kaddamar dashi, kuma ya duba irin kayan aiki na zamani da gwamnatin jihar Kano ta zuba a ciki.

Wani bawan Allah mazaunin jihar ta Kano yace ko ba komai yaji dadin zuwan shugaba Buhari Kanon domin kuwa zai kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar tayi mutanan jihar su fara cin gajiyarsu.
Daga nan kuma shugaban Kasa, Buhari yaje Asibitin titin zoo(gidan namun daji) inda nan ma ya bude asibitin kuma ya duba kayan aiki na zamani da gwamnatin jihar ta zuba a ciki.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

 Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yaje hanyar Fanshekara inda ya kaddamar da katafariyar gadarnan da gwamnatin jihar ta gina.

 Jama’a da yawane suka fito dan tarbar shugaban kasa, Muhammadu Buhari.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *